Kotu ga Gwamna Ganduje: Sai ka biya Sanusi Naira miliyan 10 bisa fatattakar sa daga Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata da ta gabata, ta bayyana cewa korar Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II, ko zuwa Jihar Nassarawa bayan an tsige shi daga sarautar Kano ya saɓa wa dokar ƙasa.

Alƙalin kotun, Anwuli Chikere, a hukuncin da ya yi , ya bayyana cewa dokar kafa Masarautar Kano ta 2019 da gwamnatin jiha ta kafa ta kuma yi amfani da ita wajen korar Sarki Sanusi bayan ta tsige shi ta saɓa wa kundin tsarin mulki na 1999.

Ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar nan shi ne a gaba kuma duk wata doka da a ka ƙirƙire ta ba a doron kudin ba, to ba abar karɓa ba ce.

Alƙalin ya ƙara da cewa tsohon sarkin na Kano yana da ‘yancin da zai zauna a ko’ina a faɗin ƙasar nan har da ma Jihar Kano.

Kamfanin Daillancin Labarai, NAN ya rawaito cewa bayan da a ka tsige sarkin a ranar 9 ga watan Maris, 2020, sai ya kai ƙarar Shugaban ‘Yan Sanda na Ƙasa, Shugaban DSS na ƙasa, tun a ranar 12 ga watan Maris, 2020 inda ya ke ƙalubalantarsu a kan cewa an tsare shi ba bisa haƙƙin sa ba.

Haka kuma a cikin waɗanda ya kai ƙarar har da Antoni-Janar na jiha da na ƙasa.

Saboda haka alƙalin ya umarci masu ƙara na 1 da na 2 da 3 su biya Sarkin Naira miliyan 10 da kuma ba shi haƙuri ta kafafen yaɗa labarai.

Da ya ke martani a kan wannan hukuncin, Antoni-Janar na Jihar Kano, Mohammed Lawan ya bayyana cewa sun ji hukuncin kuma za su yi nazari a kai.

Da ya ke ganawa da manema labarai, Lawan ya ce gwamnatin jiha ta yi daidai da ta tsige Sarki Sanusi saboda ya sa ƙafa ya rushe al’adar Masarautar Kano.