Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar dakatar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Daga BELLO A. BABAJI

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta ƙi amincewa da buƙatar wani ɓangare na jami’yyar NNPP da ke neman a dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka shirya yi a ranar 26 ga watan Oktoba, 2024.

Waɗanda suka shigar da ƙarar sune NNPP da Injiniya Muhammad Babayo inda suka nemi kotun ta umarci Hukumar zaɓe ta jihar da Sufeton ƴan sanda da hukumar DSS su dakatar da yin zaɓen har sai an yi shari’a game da wani batu da aka jingine.

Kuma sun buƙaci kotun ta umarci dukkan waɗanda aka zayyano a matsayin waɗanda aka shigar da su ƙara da su kiyaye umarnin kotun har sai an kammala shari’ar da aka jingine.

Saidai a lokacin da ya ke hukunci kan ƙarar, Mai Shari’a Simon A. Amobeda, ya ƙi amincewa da buƙatar yin hakan, ya na mai cewa akwai buƙatar a sanar da waɗanda aka shigar ƙarar kan dalilan da suka sanya ake neman dakatar da gudanar da zaɓen a lokacin da aka tsara shi.

Alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Oktoba don yin hukuncin ƙarshe game da batun.