Kotu ta ƙwace kujerar ɗan majalisa daga hannun NNPP ta bai wa APC a Kano

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe a Jihar Kano ta tsige Yusuf Umar Datti na Jam’iyyar NNPP a matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam a jihar.

Bayan tsige Datti daga kujerar ɗan majalisa tmda ta yi, kotun ta ayya abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Musa Ilyasu Kwankwaso, a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan da ta kama Datti da laifin ƙin ajiye aikin gwamnati a tsakanin kwana 30 kafin shiga zaɓe kamara yadda doka ta tanada.

Kafin shiga zaɓen, ɗan siyasar ma’aikaci ne a Jami’ar Bayero ta Kano.

Kazalika, Alƙali Azingbe ya ce Datti ya gaza gamsar da kotun kan cewa shi ɗan jam’iyyar NNPP ne.

Kwankwaso kwamishina ne a tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *