Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Babban Kotun Tarayya a Jihar Katsina, ƙarƙashin Mai shari’a Abbas Bawale, ta ɗage ƙarar da PDP ɓangaren Mustapha Inuwa ya shigar wanda ke ƙalubalantar zaɓen shugabannin jam’iyyar da tsagin Sanata Lado Ɗanmarke ya gudanar a jihar.
Lauya da ke tsaya wa ɓangaren Lado Ɗanmarke, Mista Isaac Nwachukwu ya ƙalubalanci hurumin kotun na sauraren ƙara da bangaren Mustapha Inuwa ya shigar.
Ya ce, duk ƙorafe-ƙorafen su akan zaɓen fidda gwani ne na jam’iyyar ba zaɓen shugabanni wanda harka ce ta jam’iyya.
A ɗaya ɓangaren kuma, lauyan su Mustapha Inuwa, Mustapha shiru Mahuta, ya nemi kotun da ta rushe zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka gudanar.
Ya yi zargin cewa jam’iyyar ta haɗa kai da wani jigo a jam’iyar na hana tsagin Mustapha Inuwa damar sayen fom ɗin takara balle ma su tsaya zaɓe.
Saboda haka ne ya nemi kotun ta rushe zaɓen daga matakin jiha da na ƙananan hukumomi, ya na mai cewa a dawo ayi zaɓe na ainihi da zai ba kowane ɗan jam’iya damar shiga zaɓe kamar yadda tsarin mulkin jam’iyyar ta tanadar.
Bayan sauraroi bayyanan da lauyoyin biyu suka gabatar ne sai Mai shari’a Bawale ya ɗage ƙarar zuwa 29 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci game da batun.