Kotu ta ɗage sauraron ƙarar Marafa da Buni zuwa watan gobe

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Babbar kotu ta 07 da ke zamanta a Gusau a karon farko ta bayyana shari’ar a ranar Laraba tsakanin Sanata Kabiru Garba Marafa da shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa a ƙarƙashin Mai Mala Buni ta sanya ranar 17 ga watan Fabrairu 2022, domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Alƙalin kotun, Mai shari’a Bello Kucheri ya ce kotu ta ɗage sauraron ƙarar don bai wa duk lauyoyin ɓangarorin biyu damar tattara bayanan su a gaban kotun domin ci gaba da sauraro a ranar 17 ga watan Fabrairun wannan shekara.

Sanata Kabiru Garba Marafa a cewar tawagar lauyoyin sa ƙarƙashin Barista Misbahu Salahiddeen a wata hira da manema labarai jim kaɗan bayan ɗage cigaba da shari’ar, ya ce Sanata Marafa yana ƙalubalantar shugabancin Mai Mala Buni kan rusa shuwagabannin jam’iyyar na ɓangaren shi a jihar Zamfara watannin baya.

A cewarsa, rusa shugabannin jam’iyyar APC na jihar ɓangaren Sanata Kabiru Garba Marafa a jihar da Mai Mala ya yi da cewa, ya saɓa wa tsarin mulkin ƙasa, kuma ya saɓa wa tsarin dimokuraɗiyya.

“Muna ƙalubalantar hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa kan tauye haƙƙi na Sanata Marafa a siyasance a yayin taron jam’iyyar APC na jihar da aka kammala watannin baya a gaban wannan kotu da kuma rusa shugabannin jam’iyyarsa na matakin jiha ba bisa ƙa’ida ba,” ya ce.

Barista Misbahu Salahiddeen ya roƙi kotun da cewa duka ɓangaren Matawalle da na Abdulaziz Yari da Sanata Marafa su kasance a matsayin tare da tabbatar da adalci.

“Mu fatanmu da addu’o’inmu cewa, shari’ar da ke gaban wannan kotu maigirma, ta kawar da duk wani ɓangare uku na jam’iyyar APC a gefe domin a bai wa duk wanda ke da halaltaccen katin zama ɗan jam’iyyar APC a jihar Zamfara samun ‘yanci da walwala.”

Shi ma a wata hira da manema labarai jim kaɗan bayan ɗage cigaba da shari’ar, lauyan hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa, Dakta Hassan Liman SAN, ya bayyana jin daɗinsa da ranar da kotun ta sanya don ci gaba da gudanar da shari’ar.

Dr. Liman ya ci gaba da ƙalubalantar hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa ba ta da masaniya da  wani ɓangare na jam’iyyar a jihar ta Zamfara.

“Ina so in shaida wa kowa a jihar Zamfara cewa, dangane da hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin kwamitin riƙon ƙwarya na Alhaji Maimala Buni, babu wani ɓangaren APC a jihar Zamfara sai jam’iyya ɗaya kawai,” Dr. Liman (SAN) ya nuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *