Kotu ta ɗage shari’ar rikicin fili zuwa 17 Ga Fabrairu a Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

A wata ƙara da Kamfanin Emir General Integrated Limited ya shigar da Grand Scope Construction Limited kan zargin kutse da ƙwace masa fili da ake zargin gwamnati ce ta yi ta ke kuma bada kwangila na gina katafaren garejin ababen hawa wato (Mechanic Village) da aka bai wa kamfanin na Grand scope kwangilar ginawa, Babbar Kotun Jihar Gombe ta gudanar da zama a kai.

A zamanta, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Fatima Musa, ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Fabrairu, 2025.

Da ya ke magana da manema labarai bayan zaman farko na sauraron ƙarar, lauyan da ke wakiltar mai ƙara, Barista Sulaiman Abdurrahim, ya ce Emir General Integrated Limited na neman kotu ta bada umarnin kare filin su daga mamayar da ake zargin Grand Scope Construction Limited ke yi.

Ya ce kotun ta bada umarnin hana wanda ake ƙara, wakilansa ko wasu daga cikinsu shiga filin, don gine-gine ko yin wani aiki a wurin, har sai an kammala sauraron shari’ar.

A nasa ɓangaren, lauya mai kare wanda ake ƙara, Barista Garba Bin Ali Subi, ya nuna jin daɗinsa da ɗage zaman shari’ar, yana mai cewa hakan zai bai wa tawagarsa isasshen lokaci don tsara kariya da kuma tattara hujjojin da za su gabatar a gaban kotu.

A yayin zaman, Mai Shari’a Fatima Musa ta jaddada umarnin da kotun ta bayar tun farko, wanda ya hana wanda ake ƙara gudanar da wani aiki a wurin da ake taƙaddama har sai an warware shari’ar.

Rikicin mallakar fili ya jawo hankalin jama’a a Gombe, inda ake sa ran dukkan ɓangarorin za su gabatar da hujjoji masu ƙarfi a ranar da aka tsayar domin cigaba da sauraron shari’ar.