Kotu ta ɗage shari’ar su Atiku zuwa 18 ga Mayu

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ta ɗage sauraren shari’ar ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na shugabancin ƙasa, Atiku Abubakar, suka shigar kan nasarar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya samu yayin babban zaɓen da ya gudana.

Yayin zaman kotun a ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani, Kotun ta ɗage ci gaba da sararen ƙarar ya zuwa ranar 18 ga Mayu, 2023.

Ƙorafin da suka shigar kotu mai lamba CA/PEPC/05/2023, PDP da Atiku na ƙalubalantar bayyana Tinubu da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugabancin ƙasa.

Manhaja ta rawaito cewa, an ga Atiku da kansa ya halarci zaman kotun na ranar Alhamis.