Kotu ta ɗaure Lawan shekara bakwai saboda cin-hancin $500,000

Daga UMAR M. GOMBE

Wata Babbar Kotun Abuja, ta yanke wa tosohon ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Hon Farouk Lawan, hukuncin zaman gidan yari bisa laifin karɓar cin-hanci na $500,000 daga hannun hamshaƙin ɗan kasuwar nan, wato Femi Otedola.     

Alƙaliyar kotun, Justice Angella Otaluka, ta bayyana cewa kotu ta yanke wa Hon Lawan daga Kano, hukuncin zaman gidan kaso na shekara bakwai a bisa aikata laifuka uku wanda hukumar ICP ta tuhume shi da aikatawa.

…cikakken bayani na nan tafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *