Kotu ta ɗaure ma’aikatan banki biyu kan satar kuɗaɗen mamata a Kalaba

Babbar Kotun Kalaba a jihar Cross River ta tura wasu ma’aikatan banki su biyu zuwa kurkuku bisa laifin satar miliyoyin Naira daga asusun ajiya na wasu mamata.

An ɗaure Daniel Akpan Eno da Mbuk Idongesit ne bayan da hukumar EFCC a shiyyar Uyo ta gurfanar da su a kotun da Alƙali Edem Ita Kufre ke jagoranta a Kalaba bisa tuhumar haɗa baki da kuma wawushe maƙudan kuɗaɗe daga asusun ajiya a banki na wasu mamata.

Alƙali Kufre ya yanke hukuncin ɗaurin wata uku ga Akpan da zaɓin tara na N50, 000.00, haka shi ma Idongesit da zaɓin biyan tara na N30, 000.00.

A Larabar makon jiya ne aka gurfanar da masu laifin, inda Akpan da Idongesit suka amsa aikata laifin da aka tuhume su da shi.

Sai dai na ukunsu wanda aka zarge shi da taimakawa wajen aikata laifin, wato Victor John Okon pleaded, ya musanta aikata laifin da aka tuhume shi da shi, wanda hakan ya sa kotu ta ɗage sharia’rsa zuwa ranar 10 ga Agusta.