Kotu ta ɗaure sanata shekara 7 a kurkuku saboda rashawa

Daga WAKILINMU

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Legas ta yanke wa Sanata Peter Nwaoboshi hukuncin zaman kurkuku na shekara bakwai bayan da ta kama shi da laifin almundahanar kuɗaɗe.

Haka nan, kotun ta ba da umarnin rufe wasu kamfanoni guda biyu mallakar sanatan, wato Golden Touch Construction Project Ltd da kuma Suiming Electrical Ltd, daidai da tanadin Sashe na 22 na Dokar Haramcin Almundahana ta 2021.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan  Hukumar Yaƙi da Chin-hanci da Rashawa (EFCC) ta ɗaukaka ƙara tana ƙalubalantar hukuncin da Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke na Babbar Kotun Tarayya ya yanke a ranar 18 ga Yunin 2021 inda ya wanke Sanata Nwaoboshi daga zargin wawushe kuɗaɗen gwamnati.

EFCC ta gurfanar da mutum ukun da ke kare kansu ne bisa mallakar wani gida mai suna Guinea House da ke Marine Road a Apapa, Jihar Legas, wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 805.

Hukumar ta ce kamfanin Suiming Electrical Ltd ya biya wanda ya sayar da gidan rabin kuɗi na miliyan N322 a madadin Sanata Nwaoboshi, kuma harƙallar ta shafi kamfanin Golden Touch Construction Project Ltd.

Amma a nasa hukuncin a can baya, Mai Shari’a Aneke ya ce EFCC ta gaza gabatar da shaidu da kuma ƙwararan hujjoji a kan waɗanda da take zargin.

Sai dai, a hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce alƙalin kotun ya yi kuskure wajen yin watsi da tuhumar da ake yi wa waɗanda ake ƙara.

Ta kuma bayyana cewa EFCC ta gabatar da hujjoji masu gamsarwa ga kotun da suka tabbatar da lallai waɗanda ake zargin masu laifi ne.

Sanata Nwaoboshi, shi ne Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazaɓar Delta ta Arewa.