Kotu ta ƙi amsa buƙatar Gwamnan CBN kan takarar Shugaban Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ƙi yarda da buƙatar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emiefele ta ba shi kariyar neman takarar Shugaban Ƙasa ba tare da ya sauka daga kujerarsa ba.

Mista Emiefele dai ya gabatar da buƙatar kotun ta ayyana cewa yana da damar neman takarar shugabancin a ƙarƙashin duk jam’iyyar da yake so, yayin da yake riƙe da muqamin gwamnan bankin.

Tun da farko a Litinin lauyan Emiefele, Mike Ozekhome, ya buƙaci kotun da ta amsa buƙatarsu ta bayar da umarni na wucin-gadi na hana Hukumar Zave ta Nijeriya (INEC) da Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a na Tarayya daga hana shi shiga zaɓen fitar da gwani na duk jam’iyyar da yake so.

Da yake zartar da hukunci, alƙalin kotun Ahmed Mohammed, ya ayyana cewa, maimakon haka sai dai ya umarci hukumar zaven da Babban Lauyan su bayyana a gabanta ranar 12 ga watan Mayu domin su bayar da bahasinsu kan dalilin da suke ganin kotun bai kamata ta amsa buƙatar Mista Emiefele ba.

A zaman na Litinin, lauyan gwamnan ya ce zuwa ranar Laraba 11 ga watan Mayu, wa’adin karvar takardar bayyana sha’awar yin takarar shugaban ƙasar zai ƙare.

A ainihin ƙarar da lauyan Gwamnan Babban Bankin ya gabatar ranar 5 ga watan Mayu, 2022, lauyan ya ce babu wata dokar ƙasar da ta hana Mista Emiefele takara yana riƙe da kujerar shugabancin bankin.

Ana matsa wa Mista Emefiele lamba ne da ya sauka daga muƙami tun bayan da bayanai suka bayyana na aniyarsa ta neman takarar shugabancin ƙasar a jam’iyya mai mulkin ƙasar, APC, a farkon shekarar nan.

A watan Fabrairu na shekara mai zuwa ne 2023, za a yi babban zaɓen ƙasa a Nijeriya, inda za a zaɓi wanda zai gaji Shugaba Muhammdu Buhari wanda zai kammala wa’adinsa na biyu na shekara huɗu-huɗu.