Kotu ta amince da buƙatar ASUU bisa sharaɗin malamai su koma aiki

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja, ta umarci malaman jami’o’i ƙarƙarshin ƙungiyarsu ta ASUU, da su koma bakin aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

Kotun ta ba da umarnin ne bayan da ASUU ta shigar da ƙara tana neman izinin ɗaukaka ƙara kan umarnin da Kotun Ma’aitaka ta ba ta na ta janye yaijin aikin da take yi sannan malamai su koma bakin aiki.

Kotun ta amince da buƙatar ASUU bisa sharaɗin ta yi wa Kotun Ma’aikata biyayya wajen kiyaye umarnin da ta ba ta kan ta janye yajin aikin nata.

Daga nan, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta bai wa ASUU mako ɗaya kan ta yi wa umarnin kotun farko biyayya kafin ta ɗaukaka ƙara kan haka.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka, ta ce dole ASUU ta kawo shaidar mamabobinta sun koma aiki kafin ta ɗaukaka ƙara.