Kotu ta amince da buƙatar INEC kan sake saita na’urorin BVAS

Daga BASHIR ISAH

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPC) ta bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, damar sake seta na’urorin BVAS da ta yi amfani da su a zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Yayin zaman kotun a ranar Laraba, ta ce hana INEC sake seta na’urorin zai shafi zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi da za a gudanar a gaba.

Ta yi watsi da ƙorafin da Jam’iyyar Labour da ɗan takararta Peter Obi suka yi kan yunƙurin da INEC ɗin ta yi na sake seta na’urorin BVAS da aka yi amfani da su.

Kotun ta ce, amincewa da buƙatar Obi da jam’iyyarsa tamkar ɗaure hannayen hukumar INEC ne da kuma hana ta suke nauyin da ya rataya a kanta.