Kotu ta ayyana Alia a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Binuwai

Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamnan Jihar Binuwai mai zamanta a Makurdi, ta tabbatar da Gwamna Hyacinth Alia na Jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar.

Kotun ta kuma yi watsi da ƙarar da Jam’iyyar PDP da ɗan takararta, Titus Uba, suka shigar inda suke ƙalubalabtar sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a ranar 18 ga Maris.

Shugaban alƙalan kotun, Mai Shari’a Ibrahim Karaye, ya ce kotun ba ta da hurumin sauraren ƙarar kasancewar ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar mata abu ne da ya shafi gabanin zaɓe kamar yadda yake ƙunshe a Sashe na 285 ns Dokar Zaɓe.

Kotun ta ce kamata ya yi mai ƙara ya yi ƙararsa kan abin da ya shafi rashin cancantar ɗan takarar APC da kuma tsayar da Gwamna Alia da APCn ta yi haɗi da zargin amfani da takardar bogi a kan mataimakinsa, Sam Ode a gaban INEC.

Sakamakon zaɓen gwamnan jihar kamar yadda INEC ta bayyana, ya nuna Alia ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 473,933, yayin da Uba ya rufa masa baya da ƙuri’u 223,913.