Kotu ta ba da belin Ado Doguwa

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano ta bayar da belin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa a kan naira miliyan 500.

A makon jiya ne wata Kotun Majistare da ke zamanta a Unguwar Nomansland ta Jihar Kano, ta tura Alhassan Doguwa gidan waƙafi.

A yayin zaman kotun a ranar Litinin, lauyan wanda ake zargi, Nureini Jimoh (SAN), ya gabatar da buƙatar bayar da belin wanda yake karewa a gaban Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa, bisa hujjar cewa doka ta ba shi wannan ’yanci da kuma cewa Kotun Majistare ɗin ba ta da hurimin tsare shi.

Lauya Jimoh ya gabatar da hujjar cewa tun da wanda ake tuhumar laifukansa sun danganci kisan kai da mallakar makamai ba ba bisa ƙa’ida ba, Dokokin Shari’a ba su bai wa Kotun Majistare ikon bayar da ajiyar wanda ake tuhumar a gidan kaso ba.

Bayan sauraron wannan dalilai ne, Mai Shari’a Yunusa ya bayar da belin wanda ake tuhuma a bisa sharaɗin zai gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, kuma dole ɗaya daga cikinsu ya kasance Basarake mai daraja ta ɗaya, yayin da ɗayan zai kasance Babban Sakatare a Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya ko ta jiha

Haka kuma, Aƙalin ya umarci wanda ake zargin da ya kawo wa kotu dukkan takardunsa na neman izini tafiye-tafiye, waɗanda an yi masa rangwamin ba shi dama a kansu idan buƙatar hakan ta taso.

Daga bisani Kotun ta yi wa Doguwa kashedin tsame hannunsa daga shiga mazaɓarsa yayin duk wata harƙalla da ta shafi zaɓen gwamna da na ’yan majalisar jiha da za a gudanar Asabar mai zuwa.