Daga BELLO A. BABAJI
Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta bada belin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello akan Naira miliyan 500 da wakilcin mutune biyu.
Hakan na zuwa ne a lokacin da tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba shi da hannu a laifuka 19 da Hukumar EFCC ta shigar akansa.
Tsohon gwamnan yana fuskantar tuhuma ne kan handame wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 80, inda ya musanta zargin da ake masa.
A lokacin da aka kira sauraron ƙarar a ranar Juma’a, lauyan dake kare ɓangaren EFCC, Kemi Pinheiro (SAN) ya sanar da kotun yunƙurin bincikensu na janye takardar farko da suka shigar kan ranar da aka sanya na gurfanar da wanda ake tuhumar.
A gefe guda kuma, lauyoyin dake kare ɓangaren Yahaya Bello ƙarƙashin jagorancin Joseph Daudu, ba su ja ba game da batun, inda Mai Shari’a Emeka Nwite ya tabbatar da buƙatar.
Lauya Duadu ya bayyana dalilan da suka sa bai halarci zaman kotu ba a baya, ya na mai tabbatar da cewa daga yanzu har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar, za su tabbatar tsohon gwamnan hallarci kowane zama da za a yi a kai.
Baya ga haka ne Alƙali Nwite ya bada belin tsohon gwamnan, amma kuma zai cigaba da zama a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin da za a kammala cike ƙa’idodin belin.