Kotu ta bada umarnin ƙwace motocin gwamnati da Bello Matawalle ya yi awon gaba da su

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Sakkwato ta yi watsi da ƙarar da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya shigar game da mallakar motocin gwamnati da ya yi awon gaba da su.

A watan Yunin da ya gabata ‘yan sanda a Jihar Zamfara suka kai samame gidan tsohon Gwamna Matawalle inda suka ƙwace motocin gwamnati da ke jibge a gidan bisa umarnin kotu.

Sanarwa daga Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ta ce Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Sakkwato ta yi watsi da iƙirarin Bello Matawalle kan cewa motocin da ake magana mallakinsa ne.

A cewar Idris, Matawalle da muƙarrabansa sun yi awon gaba da baki ɗaya motocin gwamnati mallakar gwamnatin jihar ba tare da sun bar wa gwamnati mai ci komai ba.

Sanarwar ta ce, “Za a iya tuna cewa a watan Yuni, Gwamnatin Jihar Zamfara ta bai wa tsohon gwamnan jihar da mataimakinsa wa’adin kwana biyar kan su maido da baki ɗayan motocin gwamnatin da suka kwashe.

“Ganin ƙoƙarin da gwamnatin ta yi na neman a dawo da waɗannan motoci ya ci tura, ya sanya Gwamnatin Jihar Zamfara ta yanke shawarar samun umarnin kotu don ƙwato motocin, da wannan ‘yan sanda suka ƙwato sama da motoci 50.

“Bayan haka ne Bello Matawalle ya garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau. Inda kotun ta bada odar a maida masa motocin.

“Ƙari a kan haka, ya sake shigar da wata sabuwar ƙara a nan kotun yana neman kotun da ta tabbatar masa da ‘yancinsa na mallakar kadara, ciki har da motocin da ake batu.

“Gwmnatin Zamfara ta buƙaci maida shari’ar zuwa wata Babbar Kotun Tarayya ta daban mai hurumin sauraren ƙarar.

“A ranar Juma’a Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya a Sakkwato ta yi watsi da ƙarar, inda ta ƙi amincewa da buƙatar Bello Matawalle tare da yin watsi da iƙirarinsa na mallakar motoci, wanda hakan ke nuni da motocin mallakar Gwamnatin Jihar Zamfara ne.

“Gwamnatinmu ta bada himma wajen ƙwato duka kadarorin da aka yi awon gaba da su mallakin al’ummar jihar.

“Hukuncin da Babbar Kotun Tarayyar ta yanke zai ƙara mana gwiwa wajen tabbatar da adalci, sannan dukkan waɗanda suka yi rub-da-ciki kan dukiyar jihar sun fuskanci hukunci,” in ji sanarwar.