Daga BASHIR ISAH
Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, ta bai wa sashen DSS na rundunar ‘yan sandan jihar da sauran hukumomin tsaron da lamarin ya shafa umarnin su maido da motoci kimanin motoci 40 da sauran kadarorin tsohon Gwamnam Zamfara, Bello Matawalle, da suka ƙwace.
Kotun ta ce, sa’o’i 48 kacal ta bai DSS don cika wannan umarni.
Umarnin da kotun ta bayar a ranar Alhamis na zuwa ne biyo bayan samamen da jami’an DSS da na NSCDC suka kai gidajen tsohon Gwamna Matawalle a Gusau da Maradun a ranar 9 ga Yuni, inda suka kwashi motoci da sauran kadarori bisa umarnin wata ƙaramar kotu.
Da ma dai Gwamnatin Jihar ta bayyana cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar cewa, an ƙwato motoci 40 yayin samamen da jami’an tsaron suka kai.
Sai dai a cikin ƙara mai lamba FHC/GS/CS/30/2023 da lauyan Matawalle, NS Na’Ige, ya shigar Babbar Kotun Tarayya ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aliyu Bappa, ta ba da umarnin a cikin sa’o’i 48 jami’an tsaron da lamarin ya shafa su dawo da motoci da sauran kadarorin da suka kwashe a gidajen Matawallen.
Kazalika, Kotun ta sake ba da umarnin kadarorin za su kasance ƙarƙashin kulawarta ne bayan an maido da su.