Kotu ta buƙaci a yi wa Abduljabbar gwajin ƙwaƙwalwa

Kotun Shari’a a jihar Kano, ta ba da umarnin s ɗauki Sheikh Abduljabbar Nasiru-Kabara zuwa asibitin mahaukata ta Dawanau don gwajin ƙwaƙwalwarsa.

Gwamnatin Kano na tuhumar Abduljabbar ne da laifuka guda huɗu da suka shafi yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Sa’ilin zaman shari’a a ranar Alhamis, Alƙalin kotun, Malam Ibrahim Sarki-Yola, ya ba da umarnin a tafi da wanda ake zargin ya zuwa asibitin mahaukata ta Dawanau don binciken lafiyar ƙwaƙwalwarsa.

Kazalika, Alƙali Sarki-Yola a sake gudanar gwaji kan Abduljabbar a Asibitin Ƙwararru ta Murtala da ke Kano.

Daga bisani, Alƙali Sarki-Yola ya ɗage shari’ar zuwa ranar 16 ga Satumban da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *