Kotu ta dakatar da CBN aiwatar da dokar taƙaita cire kuɗi

…Ta yi barazanar tsare shugabannin bankuna

Daga BASHIR ISAH

Babban Kotu mai zamanta a Anuja, ƙarƙashin Mai Shari’a Eneojo Eneche, ta dakatar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Babban Bankin Nijeriya (CBN) da kuma wasu bankuna 27 daga aiwatar da wa’adin daina amfani da tsoffi Naira na 10 ga Fabrairu ko bayar da wani umarni saɓanin wa’adin.

Kazalika, kotun ta ba da umarnin shugabannin kotunan da lamarin ya shafa su ba da dalilin da ya sa ba za a tsare su tare da hukunta su ba saboda ɓarnar da suka yi wa fannin kuɗin ƙasa ta hanyar ɓoye sabbin Naira, wato N200, N500, da N1000 duk da CBN ya ba da kuɗin don rabar wa al’umma.

Wannan na zuwa ne bayan ƙarar haɗin gwiwar da wasu jam’iyyu biyar suka shigar kotu.

A shekarar da ta gabata Shugaba Buhari ya amince da sake wa Naira fasali lamarin da ya haifar da ruɗani da kuma ƙarancin sabbin Naira a ƙasa.

Da ma dai CBN ya ayyana 10 ga Fabrairu a matsayin wa’adin da za a daina karɓar tsoffin takardun Naira waɗanda aka sake wa fasali.

Matakin sauya fasalin Naira da CBN ya ɗauka, wasu ‘yan ƙasa na ganin hakan daidai ne yayin da wasu ke cewa bai dace ba.

A hannu guda, wasu na ganin CBN ya yi wa Buhari rufa-rufa ne kawai dangane da wannan mataki don cim ma wata ɓoyayyar manufa.