Kotu ta dakatar da Gwamnatin Tarayya daga bai wa Jihar Ribas kason kuɗi

Daga BELLO A. BABAJI

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci babban bankin Nijeriya (CBN) da ya dakatar da bai wa Jihar Ribas kason kuɗi na wata-wata da ya saba.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta bayyana hakan a yayin hukunci kan wata ƙara da Majalisar Dokokin jihar ƙarƙashin Martins Amaewhule ta shigar.

Kotun ta ce baki ɗaya kuɗin da ake bai wa gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Siminalayi Fubara daga watan Janairun 2024, abu ne wanda ya saɓa wa doka don haka wajibi ne a dakatar da shi.

Haka nan, kotun ta ce kuɗin kasafi da gwamnan ya tsara akan wasu ƴan Majalisar dokoki guda huɗu, yin karan tsaye ne wa dokar ƙasa.

Alƙalin ta kuma ce, zartar da bada kasafi ba bisa ka’ida ba, saɓa wa dokar ƙasa ne da ya yi alƙawarin bai wa kariya.

Saboda haka ne alƙalin ta haramta wa CBN da Akanta-Janar na Ƙasa da bankunan Zenith da Access sake bai wa Fubara damar sarrafa wani kuɗi daga ciki asusun ƙasa.