Kotu ta dakatar da shugabanncin PDP ɓangaren Sagagi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU Kano

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da shugabancin jam’iyyar PDP, ƙarƙashin jagorancin Shehu Wada Sagagi har sai ta gama sauraron ƙarar da aka shigar a gabanta.

Ana zargin Sagagi da biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Wani Bello Bichi ne dai ya shigar da ƙarar a gaban Mai Shari’a A. M. Bichi, inda ya yi ƙarar jami’yyar PDP da hukumar INEC da kuma sauran mutane 40.

Kotun ta ce ta bada umarnin ne domin guje wa wani yanayi da za a zama babu shugabanci a jam’iyyar, shi ya sanya ta bada umarnin ga wanda a ke ƙara na 3 har zuwa na 42.

A zantawarsa da manema labarai a Kano, Shehu Wada Sagagi ya ce za su ƙalubalancin hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na dakatar da jagorancisu, matakin na zuwa ne duk da hukuncin ƙotun Abuja na ranar 28 ga watan Afrilun da ya gabata, da ya tabbatar da shi a matsayin halataccen shugaba.

Ya ƙara da cewa: “Da hukuncin waccan kotun ta Abuja da wannan duk ɗaya ne, wato idan akwai takardar kotun wacce ke karo da juna to wacce ta fara zuwa ita ce za ta tsaya, ba ta biyu ba tunda duk matsayinsu da darajar su guda ɗaya ne, kuma lauyan nan guda ɗaya ne, shi ya sa na yanke shawarar sai mun yi ƙarar lauyan.

“Tun daga lokacin da Injiniya Kwankwaso ya fita daga Jam’iyyar PDP zuwa yanzu a gaya min me na yi na karya dokar kundin tsarin mulkin PDP?  babu shi.”

Sannan ya cigaba da cewa, “su abinda suke so na dinga zagin Dr. Rabiu Musa Kwankwaso sannan za su yadda na rabu da shi kuma ni ba haka na ke siyasa ta ba,” Inji Shehu Wada Sagagi.

Ana  dai zargin cewa Shehu Sagagi na aiki da tsohon gwamnan Kano Dr. Rabiu Kwankwaso da ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari.