Kotu ta hana Buhari da NBC rufe kafafen yaɗa labarai 53

Daga BASHIR ISAH

A ranar Litinin wata Babbar Kotu mai zamanta a Legas, ta hana Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC) ƙwace lasisi da rufe wasu kafafen yaɗa labarai 53 a faɗin ƙasa saboda rashin sabunta lasisinsu.

Wata sanarwar haɗin gwiwa mai ɗauke da sa hannun Sakatare-Janar na Ƙungiyar Editoci ta Nijeriya (NGE) Iyobosa Uwugiaren da Mataimakin Darakta na SERAP, Kola Oluwadare, ta nuna Alƙalin kotun, Akintayo Aluko ya ba da umarnin hana rufe kafafen ne bayan da ya saurari ƙorafin NGE da SERAP suka shigar kotun.

A makon da ya gabata ne NGE da SERAP suka shigar da ƙara kotu a kan Buhari da NBC, inda suka ce sashe na 10(a) na dokar NBC da hukumar ta dogara da shi wajen yi barazanar ƙwace lasisin tashohin rediyo da talabijin kimanin su 53 ya saɓa wa doka da kuma ‘yancin bayyana ra’ayi.

Don haka ɓangarorin biyu suka shigar da ƙara kotu inda suka buƙaci kotun ta dakatar da Buhari da hukumar NBC daga aiwatar da yunƙurin ƙwace lasisi da rufe kafofin da lamarin ya shafa har sai ta saurari ƙarar da ke gabanta.

Daga nan, kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 8 ga Satumban 2022.

NGE da SERAP sun shigar da ƙarar ne biyo bayan matakin da hukumar NBC ta ɗauka na barazanar ƙwace lasisin gudanarwa na kafofin yaɗa labarai 53 da kuma rufe su cikin sa’o’i 24 saboda bashin biliyan N2.6 da ta yi zargin tana bin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *