Kotu ta haramta wa NBC ƙaƙaba wa gidajen rediyo da talabijin tara

Babbar Kotu a Abuja ta ce, daga yanzu ta haramta wa Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta ci tarar gidajen rediyo da talabijin a faɗin ƙasa.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne a zaman shari’ar da ta yi a ranar Laraba.

Kazalika, da yake yanke huncin, Alƙalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya yi watsi da tarar N500,000 da NBC ta yanka wa tashohi 45 ran 1 ga Maris, 2019 a matsayin horo kan aikata ba daidai ba.

Bugu da ƙari, Alƙalin ya ce Dokar NBC da ta bai wa hukumar damar yanka tara, ta ci karo da Sashe na 6 na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa da ya ba da ikon shari’a a kotun shari’a.

Don haka ya ce kotu ba za ta naɗe hannu sannan ta zuba ido wata hukuma tana cin tara ba tare da bin doka ba.

Ya ce hukumar ba ta bi doka ba a lokacin da ta zauna a matsayin mai ƙorafi.

Tun bayan da NBC ta ƙaƙaba wa kafofin da lamarin ya shafa tarar N500,000 kowaccensu bisa zargin saɓa dokar aiki, ya sa majalisar kula da haƙƙoƙin kafafen yaɗa labarai, wato ‘Incorporated Trustees of Media Rights Agenda’, ta maka NBC a kotu a cikin ƙara mai FHC/ABJ/CS/1386/2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *