Kotu ta kori ƙarar da shugabannin Binance suka shigar kan Ribaɗu da EFCC

Wata babbar Kotu a Abuja ta kori ƙarar da binance suka shigar a kan Ribaɗu da EFCC.

Mai shari’a, Inyang Ekwo ne ya kori ƙarar sabida rashin cika ƙa’idoji. Lokacin da aka kira shari’ar domin a fara, sai a ka nemi lauyoyi masu wakiltar shugaban binance ɗin Anjarwalla a ka rasa.

Mai shari’an ya sanya 9 ga watan Yuli domin sauraren ƙarar da shi Gambaryan ya shigar.