Kotu ta kori ƙarar DSS na neman a ci gaba da tsare Emefiele

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da buƙatar da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta shigar na neman a tsawaita tsare Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Hukumar DSS ta shigar da ƙarar ne a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli, 2023, inda ta ce ta gano wasu sabbin hujjoji kan Emefiele.

Sai dai kotun ta yi watsi da buƙatar, saboda rashin hurumi.

Mai shari’a Hamza Muazu ya ce kotun majistare, ba babbar kotun ba, tana da haƙƙi na musamman na bayar da umarnin tsare mutane a ƙarƙashin sashe na 293 da 296 na dokar shari’a.

Daga baya lauyan DSS Victor Ejelonu ya janye takardar.