Kotu ta sanya N10m a matsayin belin kowane ɗaya daga masu zanga-zanga 67 da aka tsare

Daga BELLO A. BABAJI

Mai Shari’a Oboira Egwuatu ya sanya Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin belin kowane ɗaya daga cikin masu zanga-zangar tsadar rayuwa 67 cikin 76 da aka tsare.

Waɗanda aka bai wa damar belin ƴan ƙasa da shekaru 15 ne, sannan kowannen su sai ya gabatar da wani ma’aikacin gwamnati a matsayin wanda zai tsaya masa.

Baya ga waɗannan, akwai wasu matasa 87 da aka tsare kan irin laifin waɗanda galibin us ƴan Jihar Kaduna ne.

An tsare su ne da tuhumar laifuka goma da suka ƙunshi zargin hamɓarar da gwamnati da ƙoƙarin haddasa tarzoma a Nijeriya waɗanda hakan sun saɓa wa dokar ƙasa sashi na 96 da 97.

Masu zanga-zangar sun kasance cikin yanayi na rashin samun isasshen abinci inda huɗu daga cikin su suka yanki jiki yayin da ake tsaka da shari’ar inda aka gaggauta fitar da su waje.

Wasu daga cikin su sun haɗa da; Nura Ibrahim mai shekaru 24, Abdulbasi Abdusalami (34), Ahmed Yusuf (25), Awolu Abdulahi (21), Umar Musa (15), Muhammadu Mustapha (16), Umar Muhammed (23), Umar Inusa (18), Abdullahi Sani (21), Abba Usman (30), Ibrahim Rabiu (16), Abubakar San (19), Abubakar Abdullahi (18), Amir Muhammed (17), Umar Ali (17), Saminu Sani (22), Muhammed Musa (14), Suleiman Dauda (18), Ismail Abdullah (27), da Haruna Suleiman (22) da sauran su.