Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau.
Kotun Ƙolin ta tabbatar da Dr. Dauda Lawal Dare a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar Gwamna ƙarƙashin Jamiyyar PDP a zaɓen da za a gudanar ranar Asabar Mai zuwa.
Wannan na zuwa ne kwanaki huɗu kafin zaɓen gwamnanoni da na ‘yan majalisun jiha da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shirya a jihohi 36 na ƙasar nan.
Kotun Ɗaukaka Ƙara reshen Sokoto ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a ranar 6 ga watan Janairun 2023 inda ta soke zaɓen fidda gwani na Dauda Lawal-Dare a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara.
An ƙalubalanci zaɓen fidda gwani a Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, inda aka ba da umarnin sake gudanar da zaɓen na fidda gwani.
Hakazalika, an sake gudanar da zaɓen ne a ranar 23 ga Satumba, 2022 kuma Lawal-Dare ya sake lashe zaɓen amma kuma Kotun ta soke zaɓen saboda wasu kura-kurai.
Waɗanda suka shigar da ƙara, Dauda Lawal-Dare, Adamu Maina-Waziri, shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP da Kanar Bala Mande (mai ritaya) sun kai ƙarar Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ta yi musu gyara.
Waɗanda suka ƙalubalanci ƙarar a gaban kotun sun had’ɗa da Dr Ibrahim Shehu-Gusau, Alhaji Wadatau Madawaki, Hafiz Nuhuche da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
A cikin wani hukunci na bai-ɗaya da Mai s’Shari’a Abubakar Talba ya karanta a madadin wasu, Mai Shari’a Talba ya ce waɗanda suka shigar da ƙara sun yi nasarar tabbatar da dukkanin wasu dalilai guda bakwai na ɗaukaka ƙara da lauyoyin suka zayyana kuma duk sun yanke hukunci a kan waɗanda suka ɗaukaka ƙara.
Ya yi watsi da duk wasu hukunce-hukunce na farko kan cancantar ƙarar da aka shigar bisa tushen tanade-tanaden shari’a.
Mai shari’a Talba ya ce Alƙalin kotun bai yi daidai da takardun rangwamen da INEC ta miƙa ba, kuma Kotun Shari’ar ba ta ayyana lokacin sake gudanar da zaɓen da kuma sanarwar shiga zaɓen ba.
Ya ce Alƙalin da ke shari’ar ya gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ta fuskar shari’a, lamarin da ya bai wa Kotun Ƙolin damar yin watsi da shari’ar ta Kuma tabbatar da Dr Dauda Lawal Dare a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar Gwamna a ƙarƙashin Jamiyyar PDP a zaɓe mai zuwa.