Kotu ta tabbatar da nasarar da Ododo, Diri suka samu a zaɓukan Kogi da Bayelsa

Kotun Sauraren Ƙararrakin Gwamna a Jihar Kogi mai zamanta a Abuja, ta tabbatar da nasarar da Usman Ododo na jam’iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jiharda ya gudana a ranar 11 ga Nuwamban 2023.

Kwamitin alƙalan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ado Birnin-Kudu, ƙarar da aka shigar kan nasarar da Ododo ya samu ba ta da tushe, a don haka aka yi watsi da ita.

Kazalika, Kotun ta ce masu ƙarar, Jam’iyyar SDP da ɗan takararta Murtala Ajaka, zun gaza kare zargin da suke yi da hujjoji masu gamsarwa.

A wata mai kama da wannan, Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamnan Jihar Bayelsa, ya yanke hukuncin cewa, bisa halasci aka sake zaɓen Douye Diri a matsayin Gwmanan jihar.

Kwamitin alƙalan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Adekunle Adeleye, ya yi watsi da ƙarar da Jam’iyyar APC da ɗan takararta, Timipre Sylva suka shigar saboda rashin hurumin a saurare ta.

Kotunan sun yanke dukkan hukunce-hukuncen biyu ne yayin zaman sahri’ar da suka yi a ranar Litinin.