Kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Gwamnan Zamfara

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Jihar Zamfara, ta tabbatar da nasarar da Gwamnan Jihar, Dauda Lawal ya samu a babban zaɓen da ya gabata.

Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin.

Bala Idris ya bayyana hukuncin da kotun ta yanke a matsayin tabbatar da zaɓin al’ummar jihar ta Zamfara.

Dauda Lawal ya zama gwamnan Zamfara ne biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a watan Maris da ya gabata, inda ya ɗaɗa gwamana mai ci na wancan lokaci da ƙasa.

“Ba da jimawa ba Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Jihar Zamfara mai zamanta a Sakkwato, ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ya gudana ran 18 ga Maris, 2023.

“Hukuncin ba zo da mamaki ba saboda hakan ya tabbatar da zaɓin da jama’ar Zamfara suka yi.

“Gwamna Dauda Lawal ya lashe zaɓen gwamnan jihar ne da ƙuri’u 65,750.

“A sani cewa, wannan nasara ta al’ummar Zamfara ce baki ɗaya, amma ba ga Gwamna da jam’iyya kaɗai ba,” in ji Bala Idris.