Kotu ta tabbatar da zaɓen Abdulmalik Zubairu na mazaɓar Maru/Bungudu a APC

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara ta tabbatar da zaɓen Abdulmalik Zubairu a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar APC a mazaɓar Maru/Bungudu a jihar na zaɓe mai zuwa.

Ƙarar, wani da akafi sani da Abdurrahman Tumbido ne ya shigar da ita inda yake ƙalubalantar zaɓen Abdulmalik Zubairu a gaban kotun bisa zargin an tafka maguɗi, inda ya buƙaci kotun da ta soke zaɓen.

Da yake yanke hukuncin a ranar Alhamis, Alƙalin Kotun, Mai shari’a Aminu Bappa ya yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta.

Mai shari’a Bappa ya ce kotun ta yi watsi da dukkanin shaidun da mai ƙara ya gabatar a kan cewa ba za a iya shigar da su a gaban kotun ba, don haka an yi watsi da ƙarar.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman kotun, lauya mai kare wanda ke kare kansa a gaban kotun, Barista Lawal Ahmed Nahuce, ya ce kotun ta yi watsi da dukkan shaidun da mai ƙara ya gabatar mata.

A cewarsa, an yi watsi da hujjojin ne kan cewar kotun ba ta gamsu da su ba.

Ya ce, “Shaidun da mai gabatar da ƙara ya bayar a gaban kotun ba a amince da su ba, saboda haka kotu ta yi watsi da karar”.

Nuhuce ya ci gaba da cewa, da hukuncin kotun, Abdulmalik Zubairu ya zama ɗan takarar jam’iyyar APC a mazabar Maru/Bungudu a zaɓen 2023 mai zuwa.