Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan shari’ar zaɓen shugaban ƙasa

Ya zuwa ranar 6 ga Satumban 2023 idan Allah Ya kai mu, Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPT) za ta yanke hukunci game da ƙararrakin zaɓen shugabancin ƙasa da ke gabanta.

Rajistaran Kotun Ɗaukaka Ƙara, Umar Bangari ne ya tabbatar da hakan a wani shiri da tashar Channels Television ta yi da shi ranar Litinin.

Ya ce, “Kotun Ɗaukaka Ƙara na sanar da al’umma cewar za ta yanke hukunci a kan ƙararrrakin zaɓen Shugaban Ƙasa ya zuwa ranar Laraba, 6 ga Satumba 2023.”

Ƙararrakin sun haɗa ƙara mai lamba “CA/PEPC/03/2023 tsakanin Mr. Peter Gregory Obi & Anor da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa da wasu mutum 3.”

Sai kuma ƙara mai lamba “CA/PEPC/04/2023 tsakanin Allied Peoples Movement da INEC da wasu mutum 4 Ors.

“CA/PEPC/05/2023 tsakanin Abubakar Atiku & Anor da INEC da wasu mutum 2 Ors. Da zummar tabbatar da gaskiya, kuma gidajen talabijin da ke da buƙata za su iya yaɗa zaman shari’ar kai tsaye don amfanin al’umma,” in ji Rajistaran.

Ya ƙara da cewa, ba za a bari a shiga harabar kotun ba face iya waɗanda aka sahale musu shiga.