Kotu ta tsige gwamnan Ebonyi da mataimakinsa don sun sauya sheƙa zuwa APC

Daga BASHIR ISAH

A wannan Talatar Babbar Kotu mai zamanta a Abuja ta tsige gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi tare da mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe biyo bayan sauya sheƙa da suka yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Kotun ƙarƙashin Alƙali Inyang Ekwo ta ce, ƙuri’u 393,042 da Gwamna Umahi ya samu yayin zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a 2019 a jihar Ebonyi, mallakar PDP ne wanda ba zai yiwu a juya su ga APC ba.

Don haka kotun ta ce tun da su biyun sun sauya sheƙa zuwa APC, hakan na nufin sun rasa PDPn da kuma ƙuri’un da suka samu a ƙarƙashinta.

Kotun ta ƙara da cewa, duba da sakamakon zaɓen gwamnan da ya gudana, ofishin gwamnan da na mataimakinsa a jihar “sun zama na waɗanda suka shigar da ƙara kuma ba ga wata jam’iyya ba.”

A cewar kotun, “Babu wata doka da ta halasta juya ƙuri’a daga wata jam’iyya zuwa wata.”

Don haka ta ce PDP na da hurumin ƙwace ƙuri’unta da kuma muƙamin da aka ɗora su a kai albarkacin zaɓe a jihar wanda gwamnan da mataimakinsa ba su da damar juya hakan zuwa ga APC.

Bisa wannan dalili ne kotu ta bai wa Gwamna Umahi da mataimakinsa Igwe umarnin gaggawa a kan su sauka daga muƙamansu.

Haka nan, kotun ta bai wa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, umarni a kan ta gaggauta karɓar sunaye daga PDP don maye gurbin Umahi da mataimakinsa, ko kuma ta sake shirya zaɓen gwamna a jihar daidai da sashe na 177(c) na kundin tsarin mulki na 1999.

Kazalika, kotun ta haramta wa Umahi da Igwe kan cewa daga yanzu su daina bayyana kansu a matsayin gwamna ko mataimakin gwamna a jihar Ebonyi.

Wannan hukuncin ya biyo bayan ƙarar da PDP ta shigar ne a kotu kan batun sauya sheƙar da Gwamna Umahi da mataimakinsa Igwe suka yi daga PDP zuwa APC.