Kotu ta tura ɗalibin da ake tuhuma da cin zarafin Aisha Buhari gidan yari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja mai lamba 14, ta tura wani ɗalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, Aminu Mohammed zuwa gidan gyaran hali na Suleja da ke Jihar Neja bisa zargin rubutun cin zarafin Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari a shafinsa na Tuwita.

An gurfanar da ɗalibin ne a Abuja a ranar Talata 29 ga watan Nuwamba, 2022 bisa laifin zamba ta yanar gizo inda aka hana belinsa duk da cewa ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Idan ba a manta ba, Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, jami’an tsaro ne suka ɗauki Aminu, ɗalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse, a Jihar Jigawa kan wasu kalaman ɓatanci da ake zarginsa da yi wa Uwargidan Shugaban Ƙasar.

Rahotanni na cewa, uwargidan shugaban ce ta bai wa jami’an tsaro umarnin ɗauko ma ta Aminu Adamu daga Jami’ar ta Jigawa bayan ya wallafa wasu kalamai a kanta, inda ya ke cewa, “Su mama an ci kuɗin talakawa an ƙoshi”.

An bayyana cewa, an gurfanar da Aminu ne a ranar Talata a gaban Babbar Kotun Tarayya mai lamba 14 a Abuja.

Lauyan ɗalibin, CK Agu ya tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ya ke karewar a gaban wata kotu da ke Abuja, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a ba da Aminu beli amma hakan ba ta samu ba.

“Ko a zaman kotun na jiya mun sanar da alƙali cewa mun buƙaci ’yan sanda su ba da Aminu beli cikin lokaci amma ba su amsa mana cewa za su sake shi ba ko a akasin haka.”

“Akan haka muka buƙaci kotun ta ba da shi beli bisa ɗalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba.

“Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar ’yan sanda ta gabatar da buƙatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren buƙatar yau ko gobe,” inji CK Agu.

Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai ya ce “yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari buƙatar ba da shi beli.”

A cewar kawunsa, Shehu Baba-Azare, rundunar ’yan sandan ba ta sanar da ’yan uwansa game da gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Baba-Azare ya ce, “a asirce aka gurfanar da shi a kotu, ba su sanar da mu ba, mun damu matuqa da halin da yake ciki.

“Zai yi jarrabawar ƙarshe a ranar 5 ga Disamba,” inji Baba-Azare.

Tuni dai dubban mutane suka shiga tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari wanda ya tayar da ƙura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin kama shi da tsare shi ba bisa ƙa’ida ba.