Kotu ta tura ɗan gidan tsohon Shugaban Ƙasa Yar’aduwa kurkuku kan zargin halaka mutum huɗu a Yola

An ingiza ƙeyar ɗan gidan tsohon Shugaban Ƙasa, Umaru Musa Yar’adua, Aminu Yar’adua, zuwa kurkuku a Yola, jihar Adamawa bisa zargin murƙurshe mutum huɗu har lahira da mota.

Aminu Yar’adua, ɗan shekara 36, ɗalibi ne a Jami’ar Amurka da ke Nijeriya (AUN), wata kotun Majatare ƙarƙashin jagoranci Alƙali Jummai Ibrahim ta ba da umarnin a kai shi kurkuku a Alhamis da ta gabata bisa zargin kashe mutum huɗu da mota.

An maka aminu a kotu ne bisa tuhumar yin ajalin wasu mutum huɗu sakamakon mummunan tuƙin da ya yi a ranar 23 ga Yunin 2021.

Bayanan farko da ‘yan sanda suka gabatar wa kotu ta hannun ɗan sanda mai shigar da ƙara, Inspector Zakka Musa, sun nuna Aminu ya buge mutum shida sakamakon gudun wuce kima da ya yi da mota a lokacin da yake tuƙi a babbar hanyar garin Yola a ranar 23 ga Yuni, 2021.

Haka nan, bayanan sun nuna huɗu daga cikin waɗanda haɗarin ya rutsa da su sun riga mu gidan gaskiya, yayin da ragowar biyun sun ji rauni.

Rahoton ‘yan sandan ya ce duka mutum shida da Aminu ya buge, ‘yan yankin Sabon Pegi ne daga shiyyar ƙaramar hukumar Yola ta Kudu.

Waɗanda haɗarin ya rutsa da su, su ne: Aisha Umar da Aisha Mamadu da Suleiman Abubakar da Jummai Abubakar da Rejoice Annu da kuma Hajara Aliyu, wanda baki ɗayansu matasa ne.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun cewa ‘yan’uwan Aisha Umar da Suleiman Abubakar da Jummai Abubakar da suka rasu a haɗarin, sun buƙaci a biya su diyyar Naira milyan 15.

Kotu ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 19 ga Agusta 2021, tare da ba da umarnin a kai wanda ake zargin a ajiye shi a kurku ya zuwa ranar shari’ar.

Marigayi Yar’adua shi ne ya mulki Nijeriya daga Mayun 2007 zuwa Yunin 2010, inda Allah ya yi masa cikawa sakamakon fama da rashin lafiya.