Kotu ta tura DCP Abba Kyari da wasu mutum shida kurkuku

Daga BASHIR ISAH

Alƙali Emeka Nwite na Babbar Kotun Abuja ya hana belin DCP Abba Kyari a ci gaba da shari’ar da ake yi na zarginsa da badaƙalar safarar miyagun ƙwayoyi.

Kotun ta yi matsayar cewa hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta gabatar da wadatattun hujjojin da suka hana a bayar da belin babban jami’in ɗan sandan wanda aka dakatar da shi daga aiki.

Daga cikin bayanan da NDLEA ta gabatar wa kotu har da cewa ba daidai ba ne a bada belin Kyari duba da yanayin shari’ar da ke gaban kotu.

Mutum na biyu daga cikin masu neman belin wanda Mataimakin Sufurtandan ‘yan sanda ne, shi ma akwai bincike da ke gudana a kansa bisa zargin almundahana.

Buƙatar neman zuwa kula da lafiya da ya sanya waɗanda lamarin ya shafa neman beli, kotu ta ce kula da lafiyar nasu abu ne da ba zai gagari NDLEA ba.

Kazalika, kotun ta hana belin mutum na 4 da na 5 da aka gurfanar da su a gaban kotu bisa cewa NDLEA ta gabatar da bayanin manyan laifuka a kansu.

Daga bisani, ko tu ta ɗage ci gaba da wannan shari’a zuwa ranar 27 ga Afrilu mai zuwa, yayin da ta bada damar a tsare waɗanda ake zargin a gidan yari.