Kotu ta tursasa wa kamfani cigaba da biyan albashi ga korarren ma’aikaci

Daga AMINA YUSUF ALI

Wata kotun masana’antu reshen garin Fatakwal ta tursasa wa wasu kamfani mai suna, Hughes Limited da Baker Hughes Incorporated su cigaba da biyan ma’aikacinsu, Joshua Umoren albashi duk bayan sati biyu a tsahon shekaru domin biyan haƙƙoƙinsa. 

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Zainab ta yanke hukuncin a zaman kotun na ranar Juma’ar da ta gabata, bayan ta kammala sauraren shaidu daga ɓangarorin lauyoyin guda biyu. Wato na wanda ake ƙara, da na wanda yake ƙarar. 

Alƙalin ta bayyana cewa, kamfanonin ba su karya doka ba don sun sallami Josua daga aiki ba. Amma sun karya dokar aiki ta sashe na 20 a kundin mulkin Nijeriya wajen ƙin biyan sa haƙƙoƙinsa na sallama.

A cikin ƙarar da ya shigar ga kotun, Mista Josua Umoron ya bayyana wa Kotu cewa, an ɗauke shi aiki ne a shekarar 1992, sai kuma kwatsam! A ahekarar 2009 kamfanin ya damƙa masa takardar sallama daga aiki ba tare da wani bayani ba. 

Hakazalika, lauyan Mista Umoren ya bayyana cewa, tabbas kamfanin sun yi wa dokar ƙasa hawan ƙawara wajen sallamar ma’aikata ba bisa sharuɗɗan da suke a cikin takardar yarjejeniyarsu tsakaninsu da ma’aikacin nasu ba.

A nasa ɓangaren kuma, shi ma lauyan kamfanin ya bayyana wa kotu cewa, ba rana tsaka kawai aka sallami mai ƙarar daga aiki ba. Sai da aka ba shi dama ya tattauna da mai duba shi aiki. Sannan kuma bai kasance ɗaya daga mambobin wata ƙungiya ta kasuwanci ba ballantana a ce sai sun tuntuɓi ƙungiyar kafin sallamarsa ba. 

Don haka, lauyan ya nemi kotun ta yi watsi da waccan ƙarar da Mista Umoren ya shigar na neman haƙƙinsa daga wajen kamfanin.

Amma Mai Shari’a Zainab ta bayyana cewa, da ma ai mai ƙarar bai shigar da ƙarar saboda an kore shi daga aiki bagatatan ba. Ya shigar ne a kan yadda aka kore shi ba tare da biyan sa haƙƙoƙinsa ba. A don haka ta ce, kotu ta yanke wancan hukunci na dole a kan kamfanin su cigaba da biyan korarren ma’aikacin nasu duk bayan sati biyu, duk da ta sallame shi. Har sai ta biya shi dukkan haƙƙoƙinsa da suke maƙale a wuyan kamfanin.