Kotu ta umarci EFCC ta riƙe Yahaya Bello zuwa 10 ga Disamba

Daga BELLO A. BABAJI

Mai Shari’a Maryanne Anenih ta Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta ayyana ranar 10 ga watan Disamba a matsayin ranar da za ta yi hukunci game da belin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.

Ana tuhumar Bello ne tare da wani Shua’ibu Oricha da AbdulSalami Hudu akan zargin su da laifin zamba cikin aminci da almundahanar wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 110.4.

Bayan sauraron buƙatar mai kare waɗanda aka shigar ƙarar ne na a bada belin tsohon gwamnan, sai Alƙalin ta ayyana ranar gabatar da hukunci game da hakan.

An tsare Yahaya Bello ne kan wasu sabbin tuhume-tuhume guda 16 da EFCC ta gabatar wa kotun.

Daga nan ne kotun ta umarci tsohon gwamnan ya cigaba da zama a hannun EFCC.