Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya ta wanke yara matasa 71 daga Jihar Kano da aka kama bisa zargin haɗa baki wajen yin tawaye, bayan an same su da tutocin Rasha a lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance a watan Agustan 2024. Kotun babban birnin tarayya da ke Abuja ce ta yanke wannan hukunci, inda ta sallami matasan daga dukkanin tuhumar da ake musu.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kasance mai tsayin daka wajen ganin an saki waɗannan yara. Ya jaddada alƙawarin sa na amfani da duk wata hanya ta doka don tabbatar da an saki matasan. Wannan matsayi na Gwamna Yusuf ya jawo masa yabo daga ɓangarori daban-daban, musamman a wajen masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama.
Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna Yusuf, ya bayyana godiyar Gwamna ga ƙoƙarin lauyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da suka haɗa da shahararren lauya Femi Falana SAN da sauran waɗanda suka yi aiki ba dare ba rana don ganin an saki yaran. “Wannan nasara ce ga adalci da kimar ɗan Adam,” in ji Barr. Suleiman Ɗantsoho, ɗaya daga cikin lauyoyin da suka wakilci matasan.
Barrister Ɗantsoho ya yaba wa Gwamna Yusuf bisa irin goyon bayan da ya nuna ga kare haƙƙin yaran, yana mai bayyana cewa jagoranci da tsayin daka na Gwamnan ya taka rawar gani wajen ganin an samu wannan nasara. “Muna godiya ga Gwamna Abba Yusuf bisa irin goyon bayan da ya bayar wajen kare haƙƙin ɗan Adam da kimar mutanen sa,” in ji Ɗantsoho.
A yau ake sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai miƙa yaran ga Gwamna Yusuf a hukumance kafin su koma Kano ta jirgin Max Air. Wannan hukunci na kotu ya ƙara jaddada muhimmancin kare haƙƙin mutane, musamman ƙananan yara, tare da nuna ƙarfin doka wajen yaƙar rashin adalci.