Kotu ta wanke tsohon Alƙalin Alƙalai na Nijeriya, Onnoghen

Daga USMAN KAROFI

Kotun ɗaukaka ƙara ta wanke tsohon Alƙalin Alƙalai na Nijeriya, Justice Walter Onnoghen a kan tsige shi a kan muƙamin sa mai cike da cece-kuce a shekarar 2019.

Shugaban ƙasa na wancan lokacin Muhammadu Buhari ya dakatar da Onnoghen ne kwanaki kaɗan kafin zaɓen 2019, inda Tanko Muhammad ya maye gurbin sa a matsayin muƙaddashi. Wannan lamari dai ya jawo cece-kuce inda ƙungiyar lauyoyin ƙasa a lokacin su kayi Allah wadai da lamarin.

Lamarin ya ja hankali ne domin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan Onnoghen ya bayyana alƙalan da zasu jagoranci ƙararrakin zaɓen na wannan shekarar.

Bayan tsige shi ba da jimawa kotun ɗa’ar ma’aikata ta zargi Onnoghen da bayyana kadarorin ƙarya wanda hakan ya saɓawa doka.

Sai dai a wani hukunci da Mai Shari’a Bello Muhammad ya jagoranta tare da wasu alƙalai biyu sun wanke tsohon Alƙalin Alƙalan tare da umartar gwamnatin tarayya ta cire dokar hana amfani da asusun bankin shi da aka yi.