Kotu ta yanke wa ɗan hadimin Tambuwal hukunci kan yaɗa bidiyon tsiraici

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Wata babbar kotun Majistire da ke Jihar Sakkwato ta yanke wa wasu matasa ɗaurin shekaru huɗu a gidan kurkuku tare da zaɓin biyan tarar Naira dubu ɗari huɗu kowannen su, sakamakon samun su da aka yi wajen haɗa baki da yaɗa bidiyon tsiraicin wata budurwa da ake gab da auren ta a jihar.

Kotun ta samu matasan, Aminu Hayatu Tafida da Umar Abubakar da Mas’ud Abubakar da laifuka uku, inda ta yanke masu hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi kowannen su a gidan yari ko kuma zaɓin biyan tara.

Idan ba a manta ba a kwanakin bayao mahaifiyar wata budurwa a Sakkwato ta shigar da ƙara a kotun, bisa zargin yaɗa bidiyon tsiraicin `yarta da ake shirin bikin aurenta.

Inda bayan shafe dogon lokaci ana shari’ar kotun ta yi hukunci na ƙarshe, inda aka samu matasan da laifi kuma suka girbi abinda suka shuka.

Jim kaɗan bayan kammala zaman kotun, lauyan wacce ake ƙarar Barista Mansur Aliyu, ya bayyana wa manema labarai jin da]in su kan hukuncin kotun.

“Mun ji daɗin wannan hukuncin, Alhamdulillah, alƙali ya yi hukuncin yadda ya kamata, kuma ita da aka yaɗa hotunan tsiraicin ta ya umarci da a biyasu diyyar cin zarafin ta da suka yi da ya yi sanadiyyar lalacewar auren ta, kuma da ma laifuka uku ne aka cajesu da shi, laifi na farko na ɗaukar bidiyon tsiraicin ta, sai na biyun da ya kasance yaɗa bidiyon da suka yi a kafofin sada zumunta, da kuma na taimakawa wajen aikata laifin”, inji lauyan mahaifiyar yarinyar.

A cewar mahaifiyar yarinyar sun shafe sama da shekara guda suna ƙoƙarin nemo haƙƙin yar su.

“Lamari ne da muka shafe kusan shekara ɗaya muna ta ƙoƙarin bin haƙƙin `yar mu, an yi hukunci kuma ya zo ƙarshe, Alhamdulillah.” inji ta.

“Dama na shigar da ƙarar ne domin ya zamo izina ga sauran iyaye cewa lamarin fyaɗe ba abu ba ne da za mu yi shiru mu zuba ido akai ba, mu ɗauki matakin da ya dace domin ya zama izina ga saura, na sha matsin lamba sosai dangane da wannan shari’a, har da tsakar dare an shigo gidana don a tsorata ni, an yi min barazana, na gaya wa hukumar ‘yan sanda kuma sun tabbatar ba sata aka zo a yi ba, kuma har a ofishin kwamishinar shari’a aka kira ni, wasu baristoci biyu suka ajiye ni amma babu wani bayani mai ƙwari da suka yi, haka dai, yau a ce ana nema na a can gobe a ce in je can kuma ina zuwa, daga ƙarshe babu wani abu da ya fito”.

“Dama ana shirin yin bikinta a lokacin da suka fitar da hoton nata a shafukan sada zumunta, don haka mijin da za ta aura sai ya janye, ya ce ya fasa auren.”

A cewar ta lamarin ya jefa ‘yar ta cikin damuwa sosai a lokacin, kuma Alhamdulillah a yanzu ‘yarta ta yi aure kusan wata shida da suka gabata, kuma tana ci gaba da samun kwanciyar hankali tunda an yanke hukuncin da ya dace ga mutanen da suka ci zarafinta.