Kotu ta yanke wa magidanci hukuncin kisa a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Wata Babbar Kotun Jihar Jigawa mai zamanta a garin Gumel, ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mai suna Rabi’u Mamman.

Sanarwar Daraktan Sashin Ayyuka na Musamman da Harkokin Baƙi na Ɓangaren Shari’a na jihar Jigawa, Malam Abbas Rufa’i Wangara, ya sanya wa hannu ta ce, kotun ƙarƙashin jagoranci Mai Shari’a Abubakar Sambo Muhammad ta sami Mamman da aikata kisan kai wanda ya saɓa wa sashi na 221(B) na kundin Penal code.

Kotun ta samu Rabi’u Mamman da ke garin Medinlaban a yankin ƙaramar hukumar Gagarawa da ɓoye kansa a dajin Mashebe, inda ya yi ta dukan matarsa mai suna Lamira da sanda sakamakon taƙaddama da ta shiga tsakaninsu wadda hakan ya kai ga ta rasa ranta.

Alƙali Abubakar Sambo Muhammad ya ƙara da cewar, kotun ta saurari ƙwararan shedu biyar waɗanda suka tabbatar mata Rabi’u Mamman ya aikata laifin.

Don haka, kotun ta zartar masa da hukuncin kisa ta hanyar rataya domin ya kasance izina ga masu son aikata laifi irin wannan.