Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kotu ta yanke wa masu zamba uku hukuncin shekaru shida a gidan gyaran hali a Kano.
Masu shari’a Nasiru Saminu da Usman Na’abba na babbar kotun Jihar Kano, sun yanke wa wasu mutane uku; Almustapha Nasir, Isma’il Salisu da Yakubu Shuaibu Abdullahi hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan gyaran hali.
An yanke musu hukuncin ne bayan sun amsa laifin zamba da hukumar EFCC shiyyar Kano ta gabatar a kansu.
Mai shari’a Saminu ya yanke wa Nasir da Salisu hukunci ranar Alhamis, 6 ga watan Oktoba, 2022, yayin da mai shari’a Na’abba ya yanke wa Abdullahi hukunci ranar Laraba 5 ga watan Oktoba, 2022.
Tuni aka tisa ƙeyar waɗanda aka yanke wa hukuncin zuwa gidan gyaran hali.