Kotu ta yanke wa matashi sharar masallaci kan bai wa ɓarayi masauki

Dag WAKILINMU

Wata kotu mai zamanta a Dei-Dei, Abuja, ta yanke wa wani matashi mai suna Anas Ibrahim, hukuncin sharar masallaci na tsawon wata shida bayan kama shi da laifin bai wa ɓarayi masauki.

Wani mai suna Ibrahim da ke kasuwar kayan gwari a Zuɓa ya amsa tuhumar cewa yana ɗaya daga wani gungun ɓarayi tare da roƙon kotu ta yi masa sassauci.

Alƙalin kotun, Saminu Suleiman, ya bai wa mai laifin umarnin ya share Babban Masallacin Zuɓa na wata shida ko kuma ya biya tarar N20,000.

Tun da farko, lauyan mai gabatar da ƙara, Chinedu Ogada, ya faɗa wa kotun an tsare mai laifin ne biyo bayan bayanan da aka samu a kansa daga majiya mai tushe inda aka kai rahotonsa ofishin ‘yan sanda na Zuɓa, Abuja, a ranar 2 ga Janairu.

Ogada ya ce majiyar ta yi iƙirarin mai lafin na bai wa ɓarayi masauki da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi tare da kai wa mazauna Zuɓa hari.

Ogada ya ƙara da cewa, yayin binciken ‘yan sanda mai laifin ya amsa tuhuma.

Ya ce laifin ya saɓa wa Sashe na 30B ‘Penal Code’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *