Kotu ta yanke wa wanda ya kashe kwarton matarsa hukuncin kisa

Wata babbar kotu a Jihar Ogun ta yanke wa wani mai suna Adelake Bara hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun sa da laifin harbe wani mai suna Olaleye Oke, wanda ya kama yana yin lalata da ɗaya daga cikin matansa uku.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da mai shari’a Patricia Oduniyi ta yanke a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni, 2022, inda ta bayyana cewa, masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar da ake yi masa ba tare da wata shakka ba cewa Bara na da laifi.

Mai shari’a Oduniyi ya ce, laifin ya ci karo da dokar manyan laifuka ta Ogun.

A yayin shari’ar, lauya mai shigar da ƙara na jihar, T.O Adeyemi, babban Lauyan jihar, ya bayyana cewa, wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Mayu, 2018, da misalin ƙarfe 6 na yamma, a Afodan Farm Settlement, Ijoun, a yankin Aiyetoro a jihar Ogun.

Adeyemi ya ce, marigayin yana gonarsa ne Bara ya same shi inda ya zarge shi da neman ɗaya daga cikin matansa.

“Bara wanda ke da mata uku ya fito da bindiga ya harbe Oke a kai, yayin da shi kuma ke ƙoƙarin bayyana cewa ba shi da wata alaƙa da wasu matan Bara da ake zargi,” inji ta.

Lauyan ya ce, harbin da aka yi a kan Oke ya kai ga mutuwarsa.