Kotu ta yankewa Mubarak Bala zaman gidan yari na shekaru 24 saboda aikata laifin saɓo

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wata babbar kotu a Kano da ke arewacin Najeriya ta sake aike wa da Mubakar Bala zuwa gidan gyaran hali, saboda ci gaba da tsare rayuwarsa da kuma gazawar lauyoyinsa na gabatar wa kotun da cikakaken takardun da za su tabbatar mata cewar yana fama da rashin lafiya.

An karanto wa Mubarak Bala caji 14 da ake tuhumarsa a kai na yin saɓo.

Yayin zaman kotun, an karanto masa sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook, waɗanda ya yi kalaman batanci ga addinin Musulunci.

Mubarak ya amsa dukkannin caji 14 da aka karanto masa da cewar ya aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.

Ganin haka sai lauyansa ya roki kotun ta ba shi damar ganawa da wanda yake wakiltar, wato Mubarak Bala, kuma bayan ta amince, ya yi ƙoƙarin nuna ma sa tasirin cewa ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa.

Mubarak Bala a kotu
Amma bayan da lauyan ya sanar da kotun cewa Mubarak Bala na son sauya amsar da ya bayar a gaban kotun, sai alkalin ya sake tambayar wanda ake tuhumar ko haka lamarin yake.

Mubarak Bala ya sanar da kotun cewa ba zai sauya amsa laifinsa da ya yi a gaban kotun ba.

Alkali kotun ya tambaye shi ko ya fahimci nauyin abubuwan da yake cewa, kuma wanda ake tuhumar ya amsa cewa ya fahimci komai.

Ya ƙara da cewa babu wanda ya tursasa masa don ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa. Sannan ya ce babu wanda yayi masa wani alƙawari, ko ya sanya masa wani ra’ayi, sai dai ya buƙaci kotun ta yi masa sassauci da kuma adalci.

To sai dai kuma, daga ƙarshe mai shari’a Farouk Lawan ya yankewa Mubarak Bala hukuncin zaman gidan yari na tsahon shekaru 24.