Kotu ta yi wa APC da PDP aski

*Ta hargitsa PDP a Zamfara
*Ta dawo wa Aishatu Binani da haƙƙinta a Adamawa
*Ta bai wa Bwacha nasara a Taraba
*Ta girgiza APC a Ribas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A jiya Alhamis ne kotunan ɗaukaka qara a faxin Tarayyar Nijeriya suka yanke wasu hukunce-hukunce da suka baddala halin da manyan jam’iyyun ƙasar, APC da PDP, suke ciki a wasu jihohin ƙasar, lamarin da aka wayi garin Juma’a a na cigaba da cece-kuce a kansa.

Zamfara:

Kotun Ɗaukaka Ƙara dake zamanta a Sakkwato ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara, Alhaji Lawal Dauda Dare, ya shigar a gabanta bisa dalilan rashin cancanta.

An tattaro cewa, an shigar da ƙarar ne a farkon wannan watan na Nuwamba kuma an yi gardama ne tsakanin lauyoyin masu ƙara da waɗanda ake ƙara a ranar 18 ga Nuwamba, bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a baya, da ke zama a Gusau.

Alƙalin kotun, Mai shari’a M.L. Shu’aibu, wanda ya karanta hukuncin baki ɗaya a madadin wasu mutane biyu, ya yi watsi da ƙarar gaba ɗayansa saboda rashin cancanta.

Waɗanda suka amsa sun haɗa da Dr Ibrahim Shehu-Gusau da Alhaji Wadatau Madawaki da Hafiz Nuhuche da kuma hukumar zaƙe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

Mai shari’a Shu’aibu ya tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Zamfara ta yanke na soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayun 2022 wanda ya samar da Dare a matsayin ɗan takarar gwamna kan wasu kura-kurai.

Ya ce, waɗanda suka shigar da ƙara sun bi hukuncin ƙaramar kotu da mai shari’a Bappah-Aliyu ya yanke kuma sun shiga sabon zaɓen fidda gwani da aka yi a ranar 23 ga watan Satumba.

Ya ci gaba da cewa, halartar sabon zaɓen fidda gwani, da shedu da kuma takardun da aka gabatar a matsayin baje koli, waɗanda suka shigar da ƙara sun amince da karya dokokin zaɓe tare da gindaya ƙa’idojin PDP.

Alƙalin kotun ɗaukaka ƙarar ya ce, ya yi la’akari da duk hujjojin da lauyoyi daban-daban suka gabatar, da bayanin hukunce-hukuncen kotuna da sauran hukunce-hukuncen shari’a kuma ya kai ga yanke hukuncin inda ya yi watsi da ƙarar bisa rashin cancanta da kuma tabbatar da hukuncin da ƙaramar kotun ta yanke.

Ribas:

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Fatakwal ta kori ɗan takarar gwamnan Jihar Ribas na jam’iyyar APC, Tonye Cole, saboda samunsa da shaidar zama ɗan ƙasa biyu mabambamta da kuma karan-tsaye da jam’iyyarsa ta yi wa Dokar Zaɓe.

Jam’iyyar PDP a jihar ce ta garzaya kotu domin a bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) umarni qin amincewa da Tonye Cole a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC bisa zargin yana da shaidar ɗan ƙasa guda biyu.

PDP ta kuma yi zargin cewa wakilian jam’iyyarsa ba su bi ƙa’ida ba wajen zaɓarsa.
Alƙalin kotun, mai shari’a Emmanuel Obile a hukuncin da ya yanke, ya amince da batun jam’iyyar PDP cewa Cole wanda ke da shaidar ɗan ƙasa biyu bai cancanci tsayawa takarar gwamna ba da kuma zacen fidda-gwanin jam’iyyar APC da ya kawo shi.

Tuni kotun ta bai wa jam’iyyar umarnin sake wani zaɓen fidda-gwanin a jihar.

Adamawa:

A ɗaya ɓangaren kuma, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Yola ta mayar da Sanata Aishatu Ahmed Binani a matsayin ’yar takarar gwamnan Jihar Adamawa a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Hukuncin guda uku da babban alƙalin kotun Tani Yusuf Hassan ya karanta a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, 2022, ya yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Yola ta yanke, wadda ta kori Binani.

Don haka kotun ɗaukaka ƙara ta umarci jam’iyyar APC da ta sake miƙa sunan Binani ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a matsayin ’yar takarar gwamna.

Idan za a iya tunawa cewa, a ranar 14 ga Oktoba, 2022, wata babbar kotun tarayya da ke Yola ta soke zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC wanda ya samar da Binani a matsayin ’yar takarar gwamna na jam’iyyar.

Mai shari’a Abdul-aziz Anka ya bayyana cewa ba shi da tushe balle makama a zaɓen da jam’iyyar APC ta gudanar a ranar 26 ga watan Mayun 2022, sannan ta soke zaɓen da aka ce Binani ya yi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Don haka ya bayyana cewa APC ba za ta iya tsayar da kowane ɗan takara a zaɓen 2023 ba.

Sai dai alƙalin kotun ɗaukaka ƙara, Hassan ya bayyana cewa ƙarar da aka shigar ta hanyar sammacin ta taho ne zuwa kotun ɗaukaka ƙara da batutuwa takwas domin tantancewa, tare da tambayoyi biyu.

Don haka ta bayyana cewa biyar daga cikin takwas an yi watsi da su yayin da sauran ukun aka warware su a madadin mai ƙara (Binani).

Tsohon shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Nuhu Ribadu, wanda ya zo na biyu a zaɓen, ya maka Binani da INEC a gaban babbar kotu, bisa zargin saye ƙuri’u da jerin sunayen wakilai ba bisa ƙa’ida ba a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 27 ga Mayu, 2022.

Taraba:

A wani labarin kuma, Kotun Daukaka Ƙara ta tabbatar da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Taraba na jam’iyyar APC.

Da suke yanke hukunci a zaman da aka yi a Yola, a ranar Alhamis, kwamitin alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Tani Yusuf Hassan, ta bayyana Bwacha a matsayin wanda ya dace ya tsaya takara a Jam’iyyar APC.

Kotun ta bayar da umarnin miƙa sunansa ga Hukumar Zaɓe ta Qasa (INEC) a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar APC a zaven 2023.

A baya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke zaven Bwacha a matsayin ɗan takarar gwamna, inda ta ƙalubalanci zaven da aka gudanar na fidda-gwani a watan Mayu, 2022.

Kotun da ke sauraren ƙarar ta saurari ƙarar da ake yi na soke zaɓen Bwacha bisa hujjar cewa zaɓen bai bi dokar zaɓe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima ba.