Kotu ta yi watsi da ƙarar da Buhari ya shigar yana ƙalubalantar ‘yan majalisa a kan dokar zaɓe

Daga AMINA YUSUF ALI

Kotun ƙoli ta Nijeriya ta yi watsi da ƙarar da Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari da Antoni Janar na Tarayya suka shigar suna ƙalubalantar ‘yan majalisa a kan dokar sashe na 84(12) na dokar zaɓe a ƙasar nan.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai wato 24 ga watan Yunin 2022, Babbar kotun ta bayyana cewa, bayan duba zuwa ga dokar da aka tabbatar da ita cikin watan Fabrairu na shekarar 2022 da muke ciki, ta ce ba ta da hurumin da za ta iya ƙalubalantar matsayin dokar zaɓen a Shari’a.

A cikin hukuncin da Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emmanuel Akomaye Agim ya gabatar, ya bayyana cewa, shigar da ƙarar da Buhari ya yi babban cin zarafi ne ga kotun.

A cewar kotun, wannan tufka da warwara da Buhari yake ƙoƙarin yi a lokaci guda wani nau’i ne na yawo da hankalin kotu wanda sam bai kamata kotu ta ƙyale ba. Hakazalika, a cewar kotun, sam shugaba Buhari ba shi da wani hurumin da Shari’a ta ba shi dama ya tsoma baki a harkar samar da dokoki. Sannan kotun ta bayyana cewa, tunda dai Buhari tuni ya riga ya ba da amincewarsa wajen samar da waccan doka ta zaɓe, to kuwa ba shi da iko a shari’ance kuma ya zo ya ƙalubalanci wannnan dokar.

Idan za a iya tunawa, dai Buhari da Abubakar Malami sun taɓa shigar da ƙara kotun ƙolin Nijeriya kan ƙalubalantar wata dokar zaɓe da ba ta yi masa ba ta 2022. Sun shigar da ƙarar ne a watan Afrilu shekarar 2022 da muke ciki kuma sun yi ƙarar majalisar dokoki ne.

Da ma dai wannan doka ta sashe na 84 (12) ta jawo ce-ce-ku-ce tun bayan da Buhari ya sanya mata hannu cikin Watan Fabrairun shekarar nan.

Sai dai bayan rattaba mata hannu kuma, shugaban ya nemi majalisar da ta shafe wannan doka daga cikin Kundin Tsarin Mulkin ƙasar nan. Amma sai ‘yan majalisar ta dokokin suka yi buris da wannan buƙata ta shugaban.

Abinda yake cikin dokar ta sashe na 84 (12) shi ne: “Babu wani zaɓaɓɓen mai riqe a muƙamin gwamnati a kowanne mataki da yake da ikon zama daliget ko ya fito a zaɓe shi a muƙamin jam’iyya ko kuma a zaɓe shi a matsayin wakilin da zai zaɓo ‘yan takara a zaɓen cikin gida a jam’iyya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *