Kotu ta yi watsi da buƙatar DSS ta neman ci gaba da tsare Godwin Emefiele

Daga BASHIR ISAH

Wata Babbar Kotu mai zamanta a birnin tarayya, Abuja, ta yi watsi da ƙarar da hukumar tsaro ta DSS ta shigar inda take buƙatar kotu ta tsawaita mata damar ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, (CBN), Godwin Emefiele.

A ranar Laraba 25 ga Yuli, DSS ta shigar da ƙarar tata a kotun, inda ta yi iƙirarin cewa ta samo ƙarin hujjar da za ta yi amfani da ita a kan Emefiele a gaban kotu.

Sai dai, Kotun ta yi watsi da ƙarar ta DSS saboda rashin hurumin sauraron ƙarar.

Alƙalin kotun, Hamza Muazu, ya ce Kotun Majastare ce ke da ikon ba da umarnin tsarewa amma ba Babbar Kotu ba.

Ya ƙara da cewa, Sashe na 293 da 296 na Dokar Shari’ar Manyan Laifuka su ne suka bai wa Kotun Majastaren ikon hakan.

Daga bisani, lauyan DSS, Victor Ejelonu, ya janye buƙatar da suka gabatar wa kotun suna nema.

A ranar Talata Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Legas ta ba da belin Emefiele kan kuɗi Naira miliyan 20, inda DSS ta sake tasre shi jim kaɗan bayan haka.