Kotu ta yi watsi da buƙatar INEC ta neman sauya damar bincikar kayan zaɓen da aka ba wa su Atiku

Daga BASHIR ISAH

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi watsi da buƙatar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta neman a dakatar da damar da aka bai wa ‘yan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi, bincikar kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa.

A ranar Juma’ar da ta gabata kotu ta bai wa Atiku da Obi damar bincikar kayan zaɓe bayan da suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar da Bola Tinubu na Jam’iyyar APC ya samu ta lashe zaɓen.

Atiku da Obi sun nuna rashin gamsuwarsu da sakamakon zaɓen inda suka yi zargin an tafka maguɗi a zaɓen.

A ranar 1 ga Maris INEC ta ayyana ɗan takarar APC, Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓe, amma ‘yan takarar jam’iyyun PDP da LP sun ce ba su yarda da sakamakon zaɓen ba.

Lamarin da ya sa su biyun suka garzaya kotu don ƙalubalantar sakamakon zaɓen.

Sai dai INEC, a cikin buƙatar da ta gabatar kan sanarwar da aka shigar a ranar 4 ga watan Maris, ta buƙaci kotun da ta sauya umarnin hana ta yin amfani da kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen.

Hukumar ta ce tana buƙatar sake saita na’urorin BVAS don amfanin zaɓe na gaba.

Sai dai kuma a hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, kotu ta ce babu buƙatar INEC ta shigar da buƙatarta saboda babu inda kotun ta bai wa Atiku, Obi da jam’iyyunsu damar bincikar rumbun tattara bayanan INEC da ma na’urorin BVAS.